FIFA: FA ta marawa Infantino baya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hukumar FA dai ta fara marawa Michel Platini baya kafin a dakatar da shi daga harkokin wasa.

BBC ta gano cewa hukumar kwallon kafar Ingila wato FA ta amince da ta marawa Gianni Infantino baya, a takararsa ta neman shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA.

Hakan dai ya biyo bayan wani taron zartarwa da hukumar gudanarwar ta FA ta yi, ranar Laraba.

Shi dai Infantino, mai shekara 45 wanda shi ne babban sakataren hukumar kwallon kafa ta turai wato UEFA, na daya daga cikin 'yan takara biyar masu neman shugabancin fifa.

Ko a baya ma, hukumar ta FA ta marawa shugaban hukumar uefa, Michel Platini, baya a takarar ta fifa, kafin a dakatar da shi daga harkokin wasanni har na shekara 8.

A ranar 26 ga Fabarairu ne dai za a yi zaben shugabancin na fifa.