PSG: Lavezzi ya koma Hebei China

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lavezzi a lokacin yana PSG

Dan wasan gaba na Paris St.Germain, Ezequiel Lavezzi ya koma kulob din Hebei China Fortune wanda ke cikin kungiyoyin da ke buga super league a kasar.

Kwantaragin dan wasan, wanda dan Argentina ne ta kare a lokacin bazara kuma an alakanta shi da komawa kungiyoyin Chelsea da Inter Milan.

Yanzu haka, Lavezzi zai hadu da tsohon dan wasan Arsenal, Gervinho da kuma dan wasan Kamaru Stephane Mbia.

A ranar 26 ne dai za a rufe kasuwar musayar 'yan wasa ta China kuma an kashe fiye da £200m a sayen 'yan wasa.

Kuma a ranar 4 ga Maris ne za a fara gasar Chinese Super League.