Hukumar kwallon Nigeria ta gargadi Oliseh

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kalaman Oliseh sun fusata wasu 'yan Najeriya

Hukumar kwallon kafa ta Nigeria, NFF ta mayar da martani ga kocin Super Eagles, Sunday Oliseh, inda ta gargade shi kan kalaman da ya yi a kwanakin baya.

Kwamitin zartarwa na NFF ya gargadi kocin yana mai cewa "Kalaman basu dace mai horar da 'yan wasan kungiyar kwallon kasar ya yi su a kafofin watsa labari ko a shafukan sa da zumunta ba."

Duk da cewa hukumar ta amince da afuwan da Oliseh ya nema, amma ta gargade shi game da kara nuna irin wannan halayyar a nan gaba.

Sai dai sanarwar NFF ta fitar ba ta yi karin bayani ba kan ko an janye yiwuwar dora wa kocin tara.

Oliseh mai shekaru 41, ya nemi afuwar hukumar ne bayan sanya wani hoton biyo da ya yi surutai na mintuna tkwas a ciki a shafinsa na intanet, inda ya bayyana masu sukansa da cewa suna hauka.