Rooney zai yi jinyar makonni shida

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sunderland ta doke Manchester United a karawarsu ta karshen mako

Dan wasan Manchester United kuma kyaftin din tawagar kwallon Ingila, Wayne Rooney zai shafe makonni shida yana jinya sakamakon raunin da ya samu a gwiwa.

Rooney ya ji raunin ne a wasan da suka buga a karshen mako tare da Sunderland, kuma hakan ya sa ba zai buga wasannin takwas da United za ta yi ba.

Kocin United Louis van Gaal ya ce "Ya zura mana kwallaye da dama saboda haka yana da muhimmanci a gare mu. Mun san da hakan sai dai babu yadda za mu yi."

Ba a sanya dan wasan mai shekaru 30 ba, a tawagar kungiyar da za su kara da kungiyar Midtjylland a gasar Europa.