Dele Alli na bukatar gogewa - Pochettino

Hakkin mallakar hoto AP

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Mauricio Pochettino ya ce Dele Alli na "bukatar gogewa" bayan ya tokari abokin karawarsa a ranar Alhamis.

Alli mai shekaru 19, ya yi wa Nenad Tomovic keta ta hanyar haurinsa da kafa bayan ya fadi kasa a wasan da Tottenham ta yi da Fiorentina da aka tashi 1-1.

Pochettino ya ce bai ga lokacin da lamarin ya faru ba, amma daga bisani bayan ya kara kallon wasan ya ce zai yi wa dan wasan tsakiyar magana.

"Akwai bukatar mu nuna masa yadda zai goge. Dan wasa ne karami saboda haka yana da abubuwan da zai koya da dama a duniyar kwallo ta wayayyu," In ji kocin.

Alli dai ya koma Tottenham ne daga kungiyar MK Dons a bara, kuma ya yi wasanni 62 ne a rukunin League one.

Pochettino ya kara da cewa "Wannan ne wasa na farko da ya yi tare da Tottenham a gasar Premier".