Championship: Bristol City ta farfado

Image caption Jonathan Kodja ya jefa kwallaye biyu a ragar MK Dons

Kungiyar wasa ta Bristol City ta samu ta dan farfado a teburin gasar Championship ta Ingila, bayan da ta doke MK Dons da ci biyu da nema, a gidanta.

Dan wasan Bristol City, Jonathan Kodjia ne ya jefa kwallaye biyu a ragar ta MK Dons.

Yanzu haka, Bristol City ce ta 20 a teburin gasar ta Championship da maki 34, a inda ita kuma MK Dons ta zama ta 21 da maki 31.

Kwallaye biyun da Jonathan Kodjia ya zura sun zama cikamakin kwallayensa 11 a gasar.