Everton ta doke Bournemouth

Hakkin mallakar hoto AP

Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta kai wasan dab da kusa da na karshe a gasar cin kofin FA cup a karo na hudu a kakkani biyar bayan kwallayen da Ross Barkley da kuma Romelu Lukaku suka saka a cikin ragar Bournemouth.

Sai dai duk da cewa Bournemouth sun samu damar buga fenality amma mai tsaron gida na Everton ya kama kwallon da Charlie Daniels ya buga.

Kwallon da Barkley ya saka a cikin ragar Bournemouth a cikin mintuna 55 da buga wasa, shi ne ya basu damar samun nasara.

A yanzu kungiyoyin za su ba shahararun 'yan wasan u damar su huta a wasannin cikin gida