'Ban ji dadin jifar da aka yi man ba' inji Brunt

Hakkin mallakar hoto Getty

Dan wasan kwallon gefe na kungiyar kwallon kafa ta West Brom, Chris Brunt ya nuna rashin jin dadinsa game da jifar da wani magoyin bayan Baggies ya yi masa da tsaba.

Brunt ya je ya mika wa daya daga cikin magoya bayansa rigar wasansa bayan da Reading ta doke West Brom da ci 3-1

''Ya ce idan mutane suna ganin zasu iya kallon wasanni kuma suna ganin abu ne mai kyau su jefi 'yan wasa ko wani da tsaba, toh sam hakan bai da ce ba," a cewar Brunt.

Hukumar kwallon kafa ta FA ta ce za ta binciki lamarin.