Man Utd ta doke Shrewsbury

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Juan Mata ne ya jefa kwallo ta biyu

Manchester United ta cancanci zuwa wasan dab-da-na-kusa-da-na-karshe na gasar cin kofin hukumar kwallon kafa ta Ingila, wato FA Cup, bayan da ta lallasa Shrewsbury da ci 3-0.

Dan wasan Man united, Chris Smalling ne ya fara daga ragar Shrewsbury. Juan Mata ne kuma ya jefa kwallo ta biyu daga bugun tazara.

Jesse Lingard ne kuma ya gara cikamakin kwallo ta ukun cikin ragar Shrewsbury.

Yanzu haka dai Shrewsbury ta fita daga gasar.