Ozil da Ramsey za su taka leda - Arsene

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ozil da Ramsey suna murna

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya ce 'yan wasan tsakiya na kungiyar, Mesut Ozil da Aaron Ramsey da mai tsaron raga, Petr Cech za su dawo wasa domin buga wasan da kungiyar tasu za ta taka da Barcelona, ranar Talata.

A wasan zagaye na biyar na gasar FA Cup dai da Arsenal din ta buga da Hull City wanda suka tashi 0-0, ba a ga 'yan wasan ba.

Arsene Wenger ya ce " dole ne mu hada cikakken rukunin 'yan wasa domin samun nasarar a kan Barcelona."

Ita ma dai kungiyar Barcelona ta dawo da dan wasanta na baya, Gererd Pique wanda yake hutu wasansu da Las Palmas da kuma dan wasan tsakiya Sergio Busquets wanda aka dakatar daga wasa.

A ranar Talata ne dai kungiyoyin biyu za su fafata a zangon wasa na daya zagaye na 16 na zakarun turai wato Champions League.