FIFA: Prince Ali yana son a dage zabe

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Dan takararar shugabancin Fifa, Prince Ali bn al-Hussain

Lauyoyin dan takarar shugabancin hukumar Fifa, Yarima Ali bin al-Hussein sun ce sun shigar da bukatarsu a hukumance ta neman a dage zaben shugabancin hukumar da za a yi, ranar Juma'a.

Ali, mai shekara 40, ya nuna rashin gamsuwarsa da tsarin zaben da aka shirya, a inda ya nemi kotun wasanni ta duniya da ta dakatar da zaben.

Kotun dai ta ce za ta saurari karar ta dan takarar, da safiyar ranar Alhamis.

Shi dai dan takarar wanda dan kasar Jordan ne yana son a gudanar da zabe sahihi kuma ba tare da kumbiya-kumbiya ba, to amma kuma hukumar zaben ta Fifa ta yi watsi da bukatar dan takarar.

Shi dai Ali yana daya daga cikin 'yan takarar shugabancin Fifa guda biyar da ke maye gurbin Sepp Blatter wanda ya kwashe shekaru 18, a kan kujerer shugabancin hukumar.