Tennis: McHale ta doke Watson

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Watson ta shaye kaye a Australian Open

'Yar wasan tennis 'yar Amurka, Christina McHale ta doke 'yar kasar Ingila mai matsayi na biyu, Heather Watson a zagaye na farko na gasar tennis ta Abierto Mexicana Telcel da ake yi a birnin Acapulco na kasar Mexico.

Watson, mai shekara 23 tasha kashi da ci 4-6 da 6-0 da 7-6.

Da ma dai 'yar wasan mai matsayi na 83 a duniya ta sha kaye a zagayen farko na gasar Australian Open, da aka yi a watan da ya gabata.

Mai matsayi na daya a wasan tennis 'yar kasar Ingila, Johanna Konta ta samu damar zuwa wasan zagaye gaba, a inda za ta kara da 'yar Croatia, Mirjana Lucic-Baroni.