Europa League: Kane ba zai buga wasa ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Harry Kane ya samu matsala a hancinsa a wasan da suka yi da Crystal Palace

Dan wasan Tottenham, Harry Kane ba zai buga wasan zango na biyu ba na gasar Europa League da kungiyar tasa za ta taka da Fiorentina, ranar Alhamis, sakamakon karaya da ya samu a hanci.

Kane, mai shekara 22 ya ji raunin ne a lokacin wasan zagaye na biyar na gasar FA Cup, da kungiyar ta buga da Crystal Palace.

A ranar Laraba ne kociyan Tottenham, Mauricio Pochettino ya ce " Muna fatan zai warware kafin ranar Lahadi, ba ya nan a yau saboda ya je ganin likita dangane da hancinsa."

Shi ma Mousa Dembele ba zai buga wasan ba saboda raunin da ya ji a cinyarsa.

A zagayen farko na gasar ta Europa an tashi 1-1 tsakanin Tottenham da Fiorentina, a Italiya, makon da ya gabata.