Ban san komai ba a kan Man Utd - Mourinho

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tun watan Disamba ne, Chelsea ta kori Jose Mourinho

Tsohon kociyan, Chelsea, Jose Mourinho ya ce ba shi da masaniya kan kasancewarsa kociyan Manchester United a nan gaba, amma kuma ya ce yana fatan dawowa harkar wasan kwallon kafa.

A farkon watan nan ne dai BBC ta rawaito cewa Manchester United ta tattauna da wakilan Mourinho.

A karshen kakar wasanni ta bana ne kwantaragin Luis van Gaal za ta kare.

A watan December ne dai kungiyar Chealsea ta kori Jose Mourinho, mai shekara 53, watanni bakwai bayan daukar kofin gasar Premeir League.