Barcelona za ta yi rawar gani - Wenger

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kociyan Arsenal, Arsene Wenger

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya ce yana da yakini kusan dari-bisa-dari cewa Barcelona za ta je ga wasan dab-da-na-kusa-da-na-karshe, a gasar zakarun turai ta Champions League.

Arsene wanda ya fadi hakan bayan da Barcelona ta lallasa kulob din nasa da ci 2 da nema, ya alakanta rashin nasarar tasu da 'yan wasansa na gaba wadanda ya bayyana da marasa sanin yadda za su zura kwallaye.

Arsene ya ce " Babbar matsalar ita ce yadda 'yan wasanmu na gaba suka kasa ci."

'Yan wasan Arsenal na gaba dai da suka hada da Alex Oxlade-Chamberlain da Olivier Giroud sun zubar da damarsu ta zura kwallaye a ragar Barcelona.