'Yar wasan England za ta koma Arsenal

Image caption Kelly Smith za ta taimakawa Pedro Martinez Losa, kociyan Arsenal a bayan fage, za kuma ta buga wasa.

Matar da ta fi kowa cin kwallaye a Ingila za ta koma kulob din Arsenal na mata.

Kelly Smith 'yar shekara 35, 'yar wasan gaba, ta sanya hannu a wani sabon kwantiragi da Arsenal na mata.

A sabon kulob din nata, Kelly za ta hada yin wasa da kuma taimakawa kociyan kulob din Pedro Martinez Losa, a bayan fage.

Sunan Kelly Smith ya fito a jerin wadanda suka cancanci kyautar gwanar wasa ta mata a shekara 2015.