Yaro ya samu kyautar rigar Messi

Hakkin mallakar hoto unicef
Image caption Murtaza Ahmadi sanye da rigar da Messi ya aiko mi shi da ita bayan ganinsa da ya yi da irinta ta leda a shafukan intanet.

Lionel Messi ya ba wani yaro kyautar rigarsa bayan da ya ga hotunan yaron a shafukan intanet sanye da rigar ta leda da aka yi da leda.

Yaron mai suna Murtaza Ahmadi dan shekara 5, daga Afghanistan, dan gani-kashe-nin fittacen dan kwallon ne, wanda soyyayarsa ta sa ya yi rigar Messin da leda, a ka kuma sa shafukan intanet.

Hotunan Murtaza sun yi farin jini, a sakamakon hakan ya sa Messin ya aika wa da yaron rigarsa ta hakika, da kuma sa hannunsa a jiki.

Messi wanda ya taba lashe kambin zakaran kwallon kafa ta duniya har sau biyar, shi ne jakadan Asusun Kanannan Yara na Majalisar Dinkin Duniya.

Image caption Murtaza Ahmadi sanye da rigarsa ta leda, mahaifinsa ya ce "ba mu da kudin za mu sayi masa rigar ta gaske".