An sa Notts County a kasuwa

Image caption Shugaban kulob din Notts County, Ray Trew ya sa kulob din a kasuwa saboda a cewarsa, ya gaji da abubuwa marasa dadi

Shugaban kulob din Notts County Ray Trew, ya ce kulob din na kasuwa.

Mista Trew ya bayyana hakan ne bayan da ya sauka daga shugabancin kulob din, sannan ya kara da cewa ya zartar shawarar yin hakan ne bayan da shi da iyalinsa ke suka sha fama da rashin kwaciyar hankali game da kulo din a 'yan kwanakin nan.

Ray Trew ya zamo shugaban kulob din ne a 2010, ya kuma nada Jamie Fullarton a matsayin kocin 'yan wasan kulob din a watan Janairu.

Kulob din ya koma na 16 a kakar wasannin da ta wuce biyu a gasar League na Biritaniya