Siasia ya sake zama kocin Super Eagles

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Siasia ya taba zama kocin Super Eagles tsakanin watan Disamba na shekarar 2010 da watan Oktoba na shekarar 2011.

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta sake nada Samson Siasia a matsayin kocin kungiyar Super Eagles.

Siasia zai yi aiki tare da Salisu Yusuf da Emmanuel Amuneke da kuma Alloy Agu domin tunkarar wasan cancantar shiga gasar cin kofin Afirka ta 2017 da za a yi a Masar.

NFF ta dauki wannan mataki ne bayan Sunday Oliseh ya yi murabus daga shugabancin Super Eagles ranar Juma'a.

Siasia ya taba zama kocin Super Eagles tsakanin watan Disamba na shekarar 2010 da watan Oktoba na shekarar 2011, kafin a soke kwangilarsa saboda ya kasa kai kungiyar matakin cancantar shiga gasar cin kofin Afirka na shekarar 2012.