Chelsea ta doke Southampton

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Cesc Fabregas, shi ya ci wa Chelsea kwallo ta biyu

Kungiyar wasa ta Chelsea ta doke ta Southampton da 2-1 a wasan mako na 27 na gasar Premier Ingila.

Da farko dai sai dai dan wasan Southampton, Shane Long ya fara jefa kwallo a ragar Chelsea, kafin tafiya hutun rabin lokaci.

Amma bayan an dawo daga hutun rabin lokaci sai dan wasan Chelsea, Cesc Fabregas ya farke, kafin Branislav Ivanovic ya kara ta biyu.

Yanzu haka dai Chelsea ta zamo ta 11 da maki 36 a teburin gasar Premeir, a inda ita kuma Southampton har yanzu tana nan a gurbinta na 7, a kan teburin.