Ana gab da sayar da Everton

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a sayar da Everton a kan £200m

Nan da wasu 'yankwanaki ana sa ran kammala sayen kulob din Everton a kan £200m.

An ce manyan masu hannun jari a kulob din kamar Kenwright sun yarda da su sayar da kaso 75 da kungiyar.

Sai dai har yanzu ba a san wa nene zai sayi kulob din ba amma ana dangata mai sayen da gabas ta tsakiya.

Tun dai a watan Nuwamban 2007, shugaban na Everton, Kenwright wanda ya sayi kulob din daga hannun Peter Johnson, a kan kudi £20m, a ranar 26 ga Disambar 1999, ya ce " idan dai har na samu mutumin da yake da niyyar sayen kulob din to zan sayar masa."

Kenwright ya dade yana fama da rashin lafiya abin da ya hana shi zuwa kallon wasanni Everton a wannan kakar wasannin.