Kai Tsaye: Bayanai kan wasanni

Latsa nan domin sabunta shafin

Barkanmu da ziyartar shafin BBC Hausa kai tsaye a kan wasanni. Za mu kawo muku labarai kan wasanni da ke faruwa a ranar Asabar musamman irin wainar da ake toyawa a nahiyar Turai dama duniya.

6:45 Wasannin gasar Premeir ta Nigeria na 28 ga Fabrairu 2016

Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Twitter
 • 4:00 Rivers United VS Ifeanyi Uba
 • 4:00 Shooting Stars VS MFM
 • 4:00 Ikorodu United VS Lobi Stars
 • 4:00 Heartland VS Abia Warriors
 • 4:00 Kano Pillars VS Wikki Tourist
 • 4:00 Enugu Rangers VS Niger Tornadoes

6:39 Wasannin gasar Bundesliga na ranar Lahadi 28 2016

Hakkin mallakar hoto Getty
 • 3:30 Augsburg VS Borussia M'gla…
 • 5:30 Borussia Dortmund VS Hoffenheim
 • 5:30 Mainz 05 VS Bayer Leverkusen
 • 7:30 Eintracht Fran…VS Schalke 04

6:34 Wasannin gasar Serie A na ranar Lahadi 28 Fabrairu 2016

Hakkin mallakar hoto AP
 • 12:30 Palermo VS Bologna
 • 3:00 Carpi VS Atalanta
 • 3:00 Sampdoria VS Frosinone
 • 3:00 Chievo VS Genoa
 • 3:00 Udinese VS Hellas Verona
 • 8:45 Juventus VS Internazionale

6:29 Wasannin gasar La Liga na ranar Lahadi 28 fabrairu 2016

Hakkin mallakar hoto AP
 • 12:00 Villarreal VS Levante
 • 4:00 Valencia VS Athletic Club
 • 6:15 Deportivo La C VS…Granada
 • 8:30 Barcelona VS Sevilla

6:25 Wasannin Premier na ranar Lahadi 28 Fabrairu 2016

Hakkin mallakar hoto Getty
 • 3:05Manchester United VS Arsenal
 • 3:05 Tottenham Hotspur VS Swansea City

5:53 Southampton 1-2 Chelsea

5:48 Branislav Ivanovic ne ya zura kwallo ta biyu a ragar Southampton

Hakkin mallakar hoto Reuters

5:45 Southampton 1-2 Chelsea

5:34 Fabregas ne ya farke wa Chelsea

Hakkin mallakar hoto epa

5:32 Southampton 1-1 Chelsea

5:29 Stoke City 2-0 Aston Villa

Hakkin mallakar hoto Reuters

5:12 Stoke City 1-0 Aston Villa

5:10 Chelsea ta canza Baba Rahman da Kennedy saboda ana ganin laifinsa ne yasa a ka zura wa Chelsea kwallo.

Hakkin mallakar hoto Getty

5:04 Mahawarar da ku ke tafkawa ta shafukanmu na sada zumunta

 • Ya'u Sule Tariwa: Up Chelsea insha Allah za muci Southampton 4 bayan half time.
 • Abubakar Sadiq Kumo: Da kyau Southampton gaskiya aikinku na kyau a cigaba da gashi.
 • Hamisu Mai Barca Sharada: Hahahahah Southampton aikinku yana kyau.
 • Abübakár Sa'ad Ganyé: Daman nasan za'a rina Chelsea ku tara a mako na gaba kawai na yau kam ba naku ba ne.
 • SaLeeh Muhammed SaLeeh Damare: Ai dama na gaya muku Southampton ba kanwar lasa, ba ce.Up Barcelona!
Hakkin mallakar hoto AP

4:59 Dan wasan Southampton, Shane Long ne ya jefa kwallo a ragar Chelsea

4:45 Southampton 1-0 Chelsea

4: 31 Har yanzu dai ba bu ci a wasannin da ake yi tsakanin Southampton da Chelsea da Leicester da Norwhich da Stoke da Aston Villa da kuma tsakanin Watford da Bournmouth

4:25 Mahawarar da ku ke tafkwa ta shafukanmu na sada zumunta

 • Abdullahi Muhammad Maiyama: Southermpton kuna sani cewa za ku hadu da gwanaye saboda haka da ku shirya da ma ka da ku shirya duk sai mun huda ragar nan. Up Chelsea.
 • Sabo Banga: Hhhhhh! Yau ma Chelsea za ki sha kashi daci 2 da , Up Ozil, Up Sanchez.
 • Umar A Umar: muna fatan Southampton ta lallasa Chelsea da ci 3-0
 • Umar Tambari Sheka: fatanmu ai raga raga da Chelsea,Up Man U!
 • Abdusshakour Ameen: Za a doke Chelsea da ci 2-1, Up man u!

4:08 'Yan wasan Chelsea: Courtois, Azpilicueta, Cahill, Ivanovic, Baba, Mikel, Fabregas, Willian, Hazard, Pedro, Costa

Hakkin mallakar hoto Getty

4:06 'Yan wasan Southampton: Forster, Cedric, Van Dijk, Fonte, Targett, Bertrand, Romeu, Clasie, Davis, Austin, Long

4:00 An take wasa tsakanin Southampton da Chelsea

3:36 Sunderland 0-1West Ham

3:32 Mahawarar da ku ke tafkawa a shafukanmu na sada zumunta.

 • Musa Sa'adu Dangamau: Fadan da ba bu ruwanka dadin kallo gare shi, Chelsea da Southampton duk wanda yayi nasara ina yi masa murna. Up Arsenal!
 • Nasiru Imam: Ai ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare. Allah ya ba wa mairabo sa'a. Mu kam up Barcarlona, ba sani ba sabo.
 • Sani Hamza Harbau: gabadai-gabada Chelsea, ba jajayen shedanu ba idan ma bakake ne to su guji haduwarmu da su, saboda mu ma yanzu mun dawo kan ganiyarmu.Up Chelsea.
 • Danfulani Yusufari: Hahaha! mai kare kama karenka damusa na yawo.Up up Chelsea.
 • Muttawakkil Gambo Doko:Hhhhh! Chelsea ruwa fa yau ya karewa dan kada dan sai Southampton ta ci 2-0.

3:31 Da karfe 4:00 ne dai agogon Najeiya da Niger za a take wasa tsakanin Southampton da Chelsea.

Hakkin mallakar hoto Getty

3:00 Sunderland 0-1West Ham an dawo daga hutun rabin lokaci

2:59 Shugaban hukumar kwallon kafa ta Ingila wato FA, Greg Dyke ya ce kasarsa za ta iya neman karbar bakuncin gasar kwallon kafa ta duniya ta 2030.

Hakkin mallakar hoto Getty

Hakan dai yana zuwa ne sakamakon nasarar da Gianni Infantino ya yi a matsayin zababben shugaban hukumar FIFA, a zaben ranar Juma'a da aka gudanar.

Hukumar kwallon kafa ta Ingilar dai ta mara wa Infantino baya a yayin zaben.

2:42 'Yan wasan West Ham: Adrian, Byram, Collins, Ogbonna, Cresswell, Noble, Kouyate, Antonio, Payet, Lanzini, Emenike

Hakkin mallakar hoto Getty

2:39 'Yan wasan Sunderland: Mannone, Yedlin, O’Shea, Kone, Van Aanholt, Kirchhoff, Cattermole, M’Vila, Khazri, N’Doye, Defoe

Hakkin mallakar hoto getty

2:34 An tafi hutun rabin lokaci

Hakkin mallakar hoto Getty

2:33 Sunderland 0-1 West Ham

2:27 Kwallon da West Ham ta zura a ragar Sunderland ta ba wa kulob din darewa mataki na biyar a teburin gasar Premier, a inda Manchester United ta fado ta shida.

Hakkin mallakar hoto Getty

2:22 Michail Antonio ya zura kwallo a ragar Sunderland

Hakkin mallakar hoto Getty

2:16 Sunderland 0-1 West Ham

1:45 An take wasa tsakanin Sunderland da West Ham.

1:44 Sam Allardyce ya sanar da 'yan wasan da za su taka masa wasa kamar haka:

Mannone, Yedlin, Kone, O'Shea (c), van Aanholt, Kirchhoff, Cattermole, M'Vila, Khazri, N'Doye, Defoe

Hakkin mallakar hoto getty

1:37 Karfe 1:45 ne dai za a take wasa tsakanin West Ham United da Sunderland.

Hakkin mallakar hoto
Hakkin mallakar hoto PA

1:27 Nan da wasu 'yan kwanaki kadan ana sa ran kammala sayen kulob din Everton a kan £200m.

Hakkin mallakar hoto Getty

An ce manyan masu hannun jari a kulob din kamar Kenwright sun yarda da su sayar da kaso 75 na kungiyar.

Sai dai har yanzu ba a san wa nene zai sayi kulob din ba amma ana dangata mai sayen da gabas ta tsakiya.

12:38 Wasannin gasar French Ligue 1 na Faransa

Hakkin mallakar hoto Getty
 • 5:00 Montpellier VS Lille
 • 8:00 Guingamp VS Angers
 • 8:00 Troyes VS Lorient
 • 8:00 Reims VS Bordeaux
 • 8:00 Toulouse VS Rennes

12:26 Wasannin gasar Bundesliga na Jamus

Hakkin mallakar hoto Getty
 • 3:30 Wolfsburg VS Bayern München
 • 3:30 Hamburger VS Ingolstadt
 • 3:30 Stuttgart VS Hannover 96
 • 3:30 Werder Bremen VS Darmstadt 98

12:24 Wasannin gasar Serie A na Italiya

Hakkin mallakar hoto Getty
 • 6:00 Empoli VS Roma
 • 8:45 Milan VS Torino

12:20 Wasannin gasar La Liga na Spaniya

Hakkin mallakar hoto Getty
 • 4:00 Real Madrid VS Atlético Madrid
 • 6:15 Getafe VS Celta de Vigo
 • 6:15 Sporting Gijón VS Espanyol
 • 8:30 Real Betis VS Rayo Vallecano
 • 10:05 Real Sociedad VS Málaga

12:17 Wasannin gasar Championship na Ingila

Hakkin mallakar hoto empics
 • 1:30 Wolverhampton … VS Derby County
 • 4:00 Blackburn Rovers VS MK Dons
 • 4:00 Bolton Wanderers VS Burnley
 • 4:00 Cardiff City VS Preston North End
 • 4:00 Charlton Athletic VS Reading
 • 4:00 Fulham VS Middlesbrough
 • 4:00 Huddersfield Town VS Ipswich Town
 • 4:00 Nottingham Forest VS Bristol City
 • 4:00 Queens Park Ra… VS Birmingham City
 • 4:00 Rotherham United VS Brentford

12:10 Wannan makon za mu kawo muku gasar mako na 27 a karawar da za a yi tsakanin Southampton da Chelsea. Za mu fara gabatar da shirin da karfe 3:30 na rana agogon Nigeria da Nijar. Za kuma ku iya bayar da gudunmawarku a lokacin da ake gabatar da shirin a dandalinmu na muhawara da sada zumunta a BBC Hausa Facebook da kuma Google +.

Hakkin mallakar hoto Getty

12:01 Wasannin gasar Premier na Ingila mako na 27

Hakkin mallakar hoto Reuters
 • 1:45 West Ham United VS Sunderland
 • 4:00 Stoke City VS Aston Villa
 • 4:00 Watford VS AFC Bournemouth
 • 4:00 Southampton VS Chelsea
 • 4:00 Leicester City VS Norwich City
 • 6:30 West Bromwich VS Crystal Palace