Rashford ne sirrin doke Arsenal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Macus Rashford ya ci kwallaye biyu a wasansa na farko na gasar Pemier

Kwallaye biyun da matashin dan wasan Manchester United, Macus Rashford ya jefa a ragar Arsenal ne suka dora Man United a kan Arsenal, a wasan da suka taka ranar Lahadi.

Rashfod wanda ya ci kwallaye biyu a wasan da ya fara bugawa Man United da ta kara FC Midtylland ranar Alhamis, shi ne dai ya fara jefa kwallo a ragar Arsenal sannan kuma ya jefa ta biyu da bugun kai.

Sai dai kuma Danny Wellbeck ya zurawa Arsenal kwallo daya bayan dawo wa daga hutun rabin lokaci. Mesut Ozil ne ci wa Arsenal kwallo ta biyu.

Har yanzu dai Arsenal ita ce ta uku a teburin Premier kuma akwai tazarar maki 5 tsakaninta da mai matsayi na daya wato Leicester, yayin da ita kuma Manchester United sun koma kan matakinsu na 5 a teburin na La Liga.

Wannan dai shi ne wasan Rashford na farko a gasar Premier.