FA tana binciken jifa da sulalla

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Shugaban hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA

Hukumar kwallon kafa ta Ingila wato FA tana binciken zargin jifa da sulalla da aka yi a wasannin Stoke da QPR, ranar Lahadi.

An yi zargin an jefi golan kulob din Stoke City, Jack Butland, da wani abu a lokacin wasansu da Aston Villa wanda aka tashi 2-1.

An ce 'yan kallo sun jefi 'yan wasan QPR a lokacin da suke murnar zura kwallaye biyu da suka yi wa Birmingham, a wasan gasar Championship.

Daman dai FA din tana bincike kan jifan dan wasan West Brom, Chris Brunt da aka yi da sulalla, a wasansu da Reading, kuma 'yan sanda tuni suka fara kame.