Ban yi wa Amurka alkawari ba - Infantino

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption sabon shugaban Fifa, Gianni Infantino da tsohon shugaban hukumar kwallon kafar turai, Uefa, Michel Platini

Sabon shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya,Fifa, Gianni Infantino ya musanta cewa alkawarin da ya yi wa Amurka ba ta bakuncin gasar kwallon kafa ta duniya ta 2026, ne yasa ya ci zabe.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Amurka, Sunil Gulati ya ba wa Infanino kuri'arsa a zagaye na biyu na zabe a lokacin zaben shugabancin Fifa ranar zabe.

Infantino ya ce " na tuntubi masu zabe da dama domin su zabe ni."

Da aka tambaye shi ko ya yi wa Gulati alkawarin karbar bakuncin gasar kwallon kafa ta duniya ta 2026, sai Infantino ya ce "a a."