Tottenham ta koma kusa da Leicester

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan Tottenham, Danny Rose yana murnar cin kwallo ta biyu

Kungiyar wasa ta Tottenham ta koma mazauninta na da wato tazarar maki biyu tsakaninta da mai matsayi na daya, a teburin Premier wato Leicester, bayan da ta doke Swansea da ci 2-1, a wasan da suka yi ranar Lahadi.

Dan wasan Swansea, Alberto Paloschi ne ya fara daga ragar Tottenham bayan da ya samu kwallon daga abokin wasansa, Jack Cork wanda shi kuma Angel Rangel ya garowa.

Nacer Chadli ne ya farke wa Tottenham bayan da Kyle Walker ya garo masa kwallon. Danny Rose ne ya jefa ta biyu.

Yanzu haka dai Tottenham tana da maki 54, abin da ya sanya ta zama ta biyu a teburin gasar Premier.