Leicester: Kante ba zai buga wasa biyu ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption N'golo Kante lokacin wasansu da Norwich wanda aka tashi 1-0 ranar Asabar

Dan wasan tsakiya na Leicester City, N'golo Kante ba zai buga wasanni biyu ba na gasar Premier sakamakon raunin da ya samu a cinyarsa.

Kante wanda ya ji raunin ranar Asabar a lokacin wasan da suka tashi 1-0 da Norwich, ba zai buga wasan da kungiyar tasa za ta taka da West Brom ba, ranar Talata da kuma wana za su buga da Watford ranar Asabar.

Sai dai kuma kociyan na Leicester, Claudio Ranieri ya ce yana da yakinin cewa Andy King zai maye gurbin Kanten.

Dan wasan mai shekara 24 wanda ya koma kulob din na Leicester a lokacin bazara, ya taka rawa a dukkannin wasannin da kungiyar tasa ta buga a wannan kakar.