Chelsea: Loftus-Cheek zai cigaba har 2021

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lotus-Cheek ya buga manyan wasanni 8 a Chelsea.

Dan wasan tsakiya na Chelsea, Ruben Loftus-Cheek ya rattaba hannu a kan wani sabon kwantaragi da kulob din nasa wanda zai kai har 2021.

Tauraruwar Loftus-Cheek, mai shekara 20, ta fara haskawa a gasar Premier a wasan da ya taka wa Chelsea a watan Janairun 2015.

Shi dai Loftus ya buga manyan wasanni takwas sannan kuma ya buga wasanni biyu na gasar zakarun turai.

Ya ce "Kulob din ya yi min duk abin da ya kamata tun lokacin da na fara a dan wasa na kasa da shekara 8, a saboda haka yanzu ina son na ramawa kura aniyarta."