Sunday Oliseh bai fadi gaskiya ba - NFF

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A watan Yulin 2015 ne dai aka nada Oliseh a matsayin kociyan Super Eagles bayan da aka kori Stephen Keshi.

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta mayar da martani ga tsohon kociyan kungiyar wasan kasar ta Super Eagles, Sunday Oliseh, dangane da maganganun da ya yi a kafafen yada labarai wadanda ya ce su ne suka sanya shi yin murabus.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce Oliseh ya bar aiki ne ba korarsa aka yi ba kuma bai sanar da hukumar ba dangane da barin aikin akalla wata daya kamar yadda ka'idojin aikinsa suka tana da.

Dangane kuma da batun da Olisen ya yi na cewa hukumar ba ta girmama shi, ta ce ba gaskiya ba ne, bilhasali ma dai shi ne ba ya girmama ta domin lokacin da hukumar ta bukaci ya rubuto mata rahota kan gasar CHAN ta Rwanda, bai yi ba.

Bisa zargin bin bashin albashi da tsohon kociyan ya yi, hukumar ta ce lokacin da aka ba shi mukamin na kociya sai da aka ba shi albashin wata uku.

Har wa yau, hukumar ta mayar da martani game da masu cewa ba a bi ka'ia ba wajen ba wa Oliseh jagorancin kungiyar wasan tun ma da farko, a inda hukumar ta ce an zabe shi ne bisa cancanta.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai Sunday Oliseh ya sanar da yin murabus daga shugabancin kungiyar Super Eagles, tuni kuma aka maye gurbinsa da Samson Siasia.