Rashford yana da basira ta daban - van Gaal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rashford a lokacin da abokan wasansa suka mamaye shi saboda da murnar zura kwallaye biyu da ya yi a ragar Arsenal.

Kociyan Manchester United, Luis van Gaal ya ce Marcus Rashford yana da basira ta musamman.

Rashford, mai shekara 18 dai ya bude ledar da ya fara takawa a gasar Premier da zura wa Arsenal kwallaye biyu daga cikin ukun da Man United din ta ci Arsenal.

Dan wasan dai ya zura wasu kwallayen biyu a ragar FC midtjylland a wasan gasar Europa League ranar Alhamis.

Van Gaal ya ce " yaran 'yan wasa suna taka rawar gani a wasanninsu na farko. Amma wasa na biyu yana kasancewa daban. To sai ga shi Macus ya zura kwallaye a duka wasannin saboda yana da basira ta musamman."

Wasu na kwatanta basirar matashin dan wasan da irin ta Patrick Kluivert da Xavi da kuma Thomas Muller.

Shi kansa kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya ce yaron ya burge shi.