Man City: De Bruyne zai dawo wasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan Manchester City, Kevin de Bruyne lokacin da ya samu rauni.

Dan wasan tsakiya na Manchester City, Kevin de Bruyne ya ce yana samun sauki kuma yana fatan dawowa yin atisaye nan da makonni biyar masu zuwa.

De Bruyne wanda shi ne yake biye wa Sergio Aguero wajen yawan zura kwallaye a wannan kakar wasannin, ya ji rauni a kokon gwiwarsa watan da ya gabata.

De Bruyne ya ce " yanzu haka an kwance min daurin saboda haka ina gab da koma wa bakin fama."

Dan wasan mai shekara 24 ya koma Man City ne daga Wolfsburg a kan kudi £55m, a watan Agusta.