Ghana: 'Muna neman Grant ya dawo'

Image caption Kociyan Black Stars, Avram Grant

Hukumar kwallon kafa ta Ghana,GFA ta nemi kociyan kungiyar wasan kasar, Avram Grant da ya koma bakin aikinsa domin ci gaba da horas da 'yan wasa.

Shi dai Grant wanda aka ba wa hutun wata daya, ya kwashe tsawon watanni uku a turai.

Ya ce ya fi son zaman turai saboda a can ne fitattun 'yan wasa bakake suke.

A 2014 ne dai aka nada Avram Grant wanda dan Isra'ila ne a matsayin kociyan Black Stars ta Ghana.