Tennis: Konta da Watson sun yi nasara

Image caption Johanna Konta ta kai ga wasan dab-da-na-kusa-da-na-karshe na gasar Australian Open.

'Yan wasan tennis guda biyu 'yan kasar Birtaniya, Johanna Konta da Heather Watson sun kai ga zagaye na biyu na gasar Monterrey Open a kasar Mexico.

Konta mai matsayi na daya a Birtaniya, ta doke 'yar Columbia, Mariana Duque-Marino da ci 6-3 da 6-3, a inda ita kuma Watson ta yi waje da 'yar Japan Misaki Doi da ci 6-4 da 6-7(0-7) da kuma 6-3.

Yanzu haka dai Konta za ta kara ne da 'yar Belgium, Yanina Wickmayer ko kuma 'yar Sweden, Johanna Larsson.

Ita kuma Watson za ta fafata da 'yar kasar Hungary, Timea Babos ko kuma Polona Hercog, 'yar Sloveni.