'Tottenham za ta iya daukar Premier'

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Claudio Ranieri ya ce Tottenham tana da karfin gaske.

Kocin Leicester Claudio Ranieri ya ce Tottenham na kan gaba a cikin kungiyoyin da za su iya daukar kofin Premier na bana.

Tottenham, wacce ke bayan kungiyar da ke gaba a gasar Premier Leicester da maki biyu a yayin da take da sauran wasanni 11, ba ta samu irin wannan dama ba tun a kakar wasa ta 2009-10.

Sai dai tsohon kocin na Chelsea, wanda a yau kungiyarsa za ta fafata da West Brom, ya yi amannar cewa Tottenham za ta kawo karshen shekara 55 da ta kwashe ba tare da daukar kofin Premier ba.

Ya kara da cewa,"Tottenham kungiya ce mai karfgin gaske a wannan karon."

Idan dai Tottenham ta yi nasara a kan West Ham a wasan da za su yi ranar Laraba, on Wednesday, sannan Leicester ta kasa doke West Brom, to Tottenham ka iya hawa saman tebirin Premier.