Leicester za ta jajirce don daukar Kofin Premier

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Claudio Ranieri ya ce Leicester za ta ci gaba da jajircewa.

Kocin Leicester Claudio Ranieri ya ce a shirye kungiyarsa take ta fafata domin ganin ta dauki Kofin Premier na Ingila na bana.

Kungiyar ce ke kan gaba a saman tebirin gasar ta Premier da maki uku bayan sun tashi da ci 2-2 a wasan da suka yi da West Brom, sai dai za ta dawo matsayi na biyu idan Tottenham ta doke West Ham ranar Laraba.

Ranieri ya ce, "Har yanzu Tottenham da Manchester City na cikin wadanda ke neman daukar Kofin kuma abu kadan Leicester za ta yi ta doke su."

Ya kara da cewa, "Muna da kwarin gwiwa. Me ya sa ba za mu dauki kofin ba? Cike muke da fata na gari."