Swansea: Guidolin yana asibiti

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Francesco Guidolin zai kwashe 'yan kwanaki a asibiti.

Kociyan Swansea, Francesco Guidolin ba zai halarci wasan da kungiyar tasa za ta taka da Arsenal ba sakamakon kai shi asibiti da aka yi saboda matsala a kirjinsa.

Guidolin, mai shekara 60 ba yana cikin yanayin mutu-kwakwai-rai-kwakwai ne ba, kuma ana sa ran nan da wasu 'yan kwanaki zai samu lafiya.

An dai kai kociyan ne zuwa asibitin kwararru kan numfashi a birnin London.

Swansea ta ce " kwararrun likitocin sun ba da shawarar cewa kamata ya yi a barshi a asibiti domin samun kulawa ta musamman ta 'yan kwanaki."

Yanzu haka, Alan Curtis ne zai kula da kulob din har zuwa lokacin da Guidolin zai samu sauki.