Liverpool ta wulakanta Manchester City

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Firmino ya zura kwallo ta uku ne jim kadan bayan fitar da Raheem Sterling.

Fatan da Manchester City ke da shi na daukar kofin gasar Premier ya fuskanci matsala bayan Liverpool ta zazzaga mata kwallo 3-0 a Anfield.

A wasan da suka buga a Wembley, City ce ta yi galaba a bugun fenareti sai dai kuma a wasan da suka buga ranar Laraba, Liverpool ce ta yi zarra.

Adam Lallana ya sa Liverpool ta fara yin nasara saboda kwallon da ya zura, yayin da James Milner ya zura kwallo ta biyu.

Roberto Firmino ya zura kwallo ta uku ne jim kadan bayan fitar da Raheem Sterling, lamarin da ya ta'azzara halin rudanin da City ta fada a ciki.

Duk da haka Man City ta yi sa'a saboda da Leicester ce kawai a cikin manyan kungiyoyi ta samu nasara a wasannin da aka yi a tsakiyar mako.

Sai dai kayen da suka sha sau uku a jere yana nufin suna bayan Leicester da maki goma.

Kazalika, dole City ta sa ido sosai a kan kungiyoyin da ke bayanta.

Yanzu haka dai Manchester United da City sun yi kankankan a maki bayan United ta yi nasara a kan Watford da ci daya mai ban haushi ranar Laraba.