An gayyaci Iheanacho a tawagar Nigeria

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Iheanacho na haskakawa a City

Dan kwallon Manchester City, Kelechi Iheanacho na daga cikin 'yan wasan da Najeriya ta gayyata domin karawa da Masar a wasan share fage na neman buga gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika da za a buga a wannan watan.

Kocin riko na Super Eagles, Samson Siasia kuma ya gayyaci dan kwallon West Ham, Victor Moses da dan wasan Arsenal, Alex Iwobi a cikin tawagar.

Siasia na rikon mukamin ne bayan da Sunday Oliseh ya yi murabus.

A ranar 25 ga watan Maris, Najeriya za ta fafata da Masar a Kaduna sannan kuma su kara a ranar 29 ga watan Maris a birnin Alexandria.

Masu tsaron gida: Carl Ikeme (Wolverhampton Wanderers, England); Daniel Akpeyi (Chippa United, SA)

'Yan wasan baya: Abdullahi Shehu (Uniao da Madeira, Portugal); Elderson Echiejile (AS Monaco, France); Kenneth Omeruo (Kasimpasa, Turkey); Godfrey Oboabona (Caykur Rizespor, Turkey); Efe Ambrose (Celtic FC, Scotland); Staneley Amuzie (Olhanense, Portugal)

'Yan wasan tsakiya: Ogenyi Onazi (SS Lazio, Italy); John Mikel Obi (Chelsea FC, England); Azubuike Okechukwu (Yeni Malatyaspor, Turkey), Victor Moses (West Ham United, England)

'Yan gaba: Ahmed Musa and Aaron Samuel (CSKA Moscow, Russia); Moses Simon (KAA Gent, Belgium); Odion Ighalo (Watford FC, England); Alex Iwobi (Arsenal FC, England); Fanendo Adi (Portland Timbers, USA), Aminu Umar (Osmanlispor, Turkey), Kelechi Iheanacho (Manchester City, England)