'Arsenal ba ta da karfin gwiwa' —Sanchez

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Alexis Sanchez na murnar cin kwallo

Alexis Sanchez ya ce Arsenal ba su da karfin gwiwar da za su ci gasar Firimiyar Ingila domin ba su yarda da kansu ba.

A hirarsa da gidan talbijin na Directv sports, Sanchez ya ce "kamata ya yi idan mun shiga fili, mu ji kamar mun ci su daya da nema", Amma ba kamar yadda kulob din ke yi a baya ba.

Arsenal ta yi watsi da damar da ta samu ta toshe tazarar da ke tsakaninta da Leicester a ranar Laraba, a lokacin da Swansea ta lallasa su da ci biyu da daya.

Kulob din ya ci kwallaye uku kacal a wasanni 11, kuma shine na uku a gasar Firimiya da maki shida a bayan kungiyar Foxes.