Premier: Tottenham ta kasa hawa saman tebir

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A lokacin wasan dai duk korar da 'yan Tottenham ba ta yin tasiri.

Tottenham ta gaza hawa saman tebirin gasar Premier bayan da ta sha kashi a hannun West Ham United a filin wasa na Upton Park.

Kwallon da Michail Antonio ya ci da kansa a minti na bakwai ce ta bai wa kungiyar nasara, dai dai 'yan WestHam sun nuna wa Tottenham cewa ruwa ba tsaran kwando ba ne.

A lokacin wasan dai duk korar da 'yan Tottenham ba ta yin tasiri.

Rabon Tottenham da hawa saman tebirin gasar Premier tun a watan Maris na shekarar 1964.