Barcelona ta zama gagara-badau

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lionel Messi ya zura kwallo 33 a kakar wasa ta bana.

Barcelona ta shafe bajintar shekara 27 a Spain bayan ta buga wasanni 35 ba tare da wata kungiya ta doke ta a kowacce gasar kwallon kafar kasar ba.

Wasan da ta doke Rayo Vallecano da ci 5-1 shi ne cikamakin wannan bajinta da kungiyar ta yi.

Lionel Messi ya zura kwallo uku a wasan, yayin da Rayo ta gaza yin katabus tun bayan kwallon farko da dan wasan Barca Ivan Rakitic ya ci.

An kori 'yan wasan Rayo, Diego Llorente da Manuel Iturra.

Manucho ne ya zura kwallon da kungiyar ta ci.

Luis Suarez da Arda Turan ne suka zura kwallo biyu, lamarin da ya sa Barcelona tserewa kungiyar Atletico da ke bi mata a saman tebirin La Liga da maki takwas.

Messi ya zura kwallo 33 a gasar ta La Liga ta bana.

Real Madrid ce ta uku a saman tebirin.