'Yar kwallo ta bayar da sadakar kwakwalwarta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mrs Chastain tana fatan bayar da kwakwalwarta zai sa a samu sauyi kan tiyata a kai.

Fitacciyar 'yar kwallon kafar Amurka Brandi Chastain, wacce ta yi tashe a Gasar cin kofin duniya na mata na shekarar 1999 , ta ce za ta bayar da sadakar kwakwalwarta ga wata Gidauniya tallafawa masu fama cutar farfadiya.

Mrs Chastain, wacce ta yi ritaya daga murza leda, ta ce tana fatan bayar da kwakwalwarta zai sa "a samu sauyi kan yadda ake gudanar da tiyata a kai".

Ta bi sahun wasu shahararrun 'yan wasan kwallon kafa da suke taimakawa wajen magance cutar farfadiya sakamakon bugun da suke yi wa kwallo da kawunansu.

An samu masu wasanni motsa jiki da dama dauke da wannan cuta.

Brandi Chastain, mai shekara 47, ta bayyana haka ne ranar Alhamis, tana mai cewa Jami'ar birnin Boston ce za ta yi amfani da kwakwalwarta domin gano dalilan da ke haddasa cutar.

A cewarta, "abin tsoro ne yadda muke dukan kwallo da ka da kuma hatsarin da hakan ka iya janyo wa, ko da ya ke ban taba fama da wannan matsala ba.".