Arsenal ta yi rawar-gani da mutum 10

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Alexis Sanchez ne ya ci wa Arsenal kwallo ta biyu.

Tun da farko dai, Dan wasan Arsenal, Aaron Ramsey ne ya fara daga ragar Tottenham kafin tafiya hutun rabin lokaci.

Dan wasan Arsenal, Francis Coquelin ya bar wasa a minti na 55 da fara wasa, bayan da ya samu yelon kati har guda biyu sakamakon ketar da ya yi wa Harry Kane.

Hakan ne yasa Toby Alderweireld ya farkewa kulob din nasa, kafin kuma Harry Kane ya jefa ta biyu to amma Arsenal ta farke ta hannun dan wasanta Alexis Sanchez.

Yanzu haka dai Tottenham tana da maki 55, a inda ita kuma Arsenal take da maki 52.