Manchester City ta lallasa Aston Villa

Image caption Sergio Aguero ne ya ci kwallaye biyu shi kadai

Kungiyar wasa ta Manchester City ta lallasa Aston Villa da ci 4-0, a wasan da suka taka da yammacin Asabar.

Dan wasan kungiyar, Yaya Toure ne dai ya fara daga ragar ta Aston Villa, kafin Sergio Aguero ya jefa ta biyu da ta uku.

Raheem Sterling ne ya samu ya saka ta hudu.

Yanzu haka Manchester City tana da maki 50 a teburin gasar Premier.