Newcastle: 'Ya kamata a kori McClaren'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kociyan Newcastle, Steven McClaren lokacin wasansu da Bournmouth

Tsohon mai kungiyar wasa ta Newcastle, Sir John Hall ya ce ya kamata a kori kociyan kungiyar, Steve McClaren saboda halin da kulob din ya tsinci kansa a ciki.

A ranar Asabar ne dai Newcastle ta zama ta 19 a teburin Premier, bayan wasan wasan da suka tashi 3-1 da Bournmouth.

Kuma wannan shi ne karo na uku a jere da kulob din yake rashin nasara, saboda haka ne Hall ya ce "akwai bukatar canji".

Hall ya kara da cewa " Steve ba ya zaburar da 'yan wasansa kuma da alama lokacin tafiyarsa ne ya zo. Ya kamata a nemi wani wanda zai dawo da martabar kulob din."

McClaren wanda ya a karkashi jagorancinsa kulob din ya yi nasara a wasanni shida kacal, a wannan kakar, ya maye gurbin tsohon kociyan kungiyar, John Carver a watan Yulin 2015.