Ronaldo v Messi: Musu ya jawo kisa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Messi ya dauki kyautar Ballon d'Or sau 5, Ronaldo kuma ya dauka sau 3.

Wani dan Najeriya mai suna Michael Chukuma ya kashe dan uwansa a kan musun wa nene ya fi wani a tsakanin dan wasan Barcelona, Lionel Messi da na Real Madrid, Cristiano Ronaldo.

'Yan sanda sun ce Chikwu, mai shekara 21, ya dabawa abokinsa, Obina Durumchukwu mai shekara 34, gilashi a wata unguwar da ke wajen birnin Mumbai.

Al'amarin dai ya faru ne da daren ranar Lahadi bayan wani taron fati da aka yi.

Insifeton 'yan sanda ya ce " suna tattaunawa a kan 'yan kwallo. Sai wanda aka kashe ya jefi wanda ake zargi da gilashi a fuska. Sai gilashin ya fashe ya kuma ji wa wanda aka jefa rauni."

Ya kara da cewa " bayan nan ne sai wanda ake zargin ya dauki fasasshen gilashin ya ji wa mamacin rauni wanda kuma ya mutu sakamakon zubar da jini da ya yi."

Shi dai Lionel Messi ya dauki kyautar dan kwallon da ya fi kowannen a duniya, Ballon d'Or har sau biyar, a inda shi kuma Ronaldo ya samu kyautar karo uku.