Muna sa ran daukar kofin Premeir - Wenger

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan dai ita ce kakar wasanni ta 20 da Arsene Wenger ya yi a Arsenal

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya ce har yanzu suna sa ran za su dauki kofin gasar Premier Ingila, duk kuwa da cewa akwai tazarar maki 8 tsakanin kulob din nasa da Leicester.

Kokarin Arsenal a gasar ya gamu da matsala ne a wasanni ukun da ta buga na baya bayan nan.

Wasan da suka taka da Tottenham wanda suka tashi 2-2 ya janyo tazarar maki uku tsakaninta da Tottenham wanda ita ce ta biyu a teburin gasar ta Premier.

Arsene Wenger ya ce duk da haka "ba za mu yi kasa a gwiwa ba, za mu ci gaba da fafatawa har zuwa karshe."

Nan gaba akwai sauran wasanni 9 da Arsenal din za ta buga.