Arsenal ta doke Hull City

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kociyan Arsenal, Arsene Wenger

Kungiyar wasa ta Arsenal ta doke Hull City da ci 4-0, a wasan neman cancantar buga wasan dab-da-na-kusa-da-na-karshe na gasar FA Cup, da suka yi da daren Talata.

Dan wasan Arsenal, Olivier Giroud ne dai ya fara zura kwallon farko a ragar ta Hull City, ana dab da tafiya hutun rabin lokaci. Olivier Giroud din ne dai ya kara jefa kwallo ta biyu.

Shi ma, Theo Wellcott ya samu ya jefa kwallaye biyu a ragar Hull City, a inda ya ci ta uku da ta hudu a jere.

Yanzu haka, Arsenal din ta cancanci zuwa wasan dab-da-kusa-da-karshe na gasar ta FA.