Illar kalaman batanci a harkar wasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kalaman baci dai yana kara yawa a harkar wasanni

An ci tarar shugaban kungiyar wasa ta Wellingborough Town a Birtaniya, Martin Potton, sannan kuma an dakatar da shi daga halartar wasanni biyar saboda kalaman batanci da ya yi a kan mace mai busa.

Ana dai zargin Potton ne da yin kalaman nuna wariya a kan rafali, Mary Harmer.

An jiyo mista Potton, a lokacin wani wasa yana cewa Mary ba za ta iya yin alkalanci a wasan mata ba ballanta ma na maza.

Sai dai kuma Potton ya musanta zargin, a inda ya ce " ina musanta duk abin da ake zargi na da shi amma dai an same ni da laifin kin zuwa kotu."