Sharapova: Shan kwaya zai zama darasi - Bollettieri

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sharapova ta ce tana fatan ba za a haramta mata wasanni ba.

Tsohon mai horas da 'yar wasan tennis, Maria Sharapova wato Nick Bollettieri ya ce gano cewa Maria tana shan kwayoyi masu kara kuzari, zai zama darasi ne ga dukkannin harkokin wasanni.

Nick Bollettieri ya shaida wa BBC cewa ya kadu da gano 'yar wasan tana shan kwaya mai kara kuzari, a inda ya ce " ta tsere saa a dukkannin abin da tasa a gaba."

Sai dai kuma kociyan mai shekara 84 ya ce "dole ne kowa ya dauki alhakin duk abin da yake yi."

Ita dai Sharapova, mai shekara 28 ta dade tana shan kwayar maganin meldonium tun shekarar 2006 saboda rashin lafiya. Sai kuma an haramta shan kwayar a 2016.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Maria Sharapova a lokacin wasan tennis

'Yar wasan dai ta bayyana cewa tana shan kwayar ne, bayan da Serena Williams ta doke ta a gasar tennis ta Australian Open, da aka yi a watan Janairu.

Yanzu haka, hukumar wasan tennis ta duniya ta ce za ta dakatar da Sharapova daga ranar 12 ga Maris.

Ana dai tunanin cewa Maria Sharapova za ta iya fuskantar haramcin wasa na tsawon shekara 4.